Al’ummar Jihar Bauchi Ku Kara Hakuri Bisa Matsalar Ruwa Da Muke Fuskanta – Kaura Media Team

 

Al'ummar Jihar Bauchi Ku Kara Hakuri Bisa Matsalar Ruwa Da Muke Fuskanta .


Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Senator Bala Muhammad Kauran Bauchi Yayi Muku Alkawarin Shawo Muku Kan Wannnan Matsalar Kamar Yadda Yafara Tun Farkon Hawansa Mulki .

Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Lokacin Daya Hau Kan Karagar Mulki Gyaran Hanyar Da Zaya Samar Da Tsaftataccen Ruwan Sha Kuma Muyi Wanka,Muyii Wanki Shi Yafara Sanyasu A Gabansa Domin Fitar Da Al’ummar Wannan Jihar Cikin Matsalar Da Suke Fuskanta Kowani Shekara.

Amma Inaso In Kara Jan Hankalin Ku Al’ummar Jihar Bauchi Kunsan Domin Shi Gyara A Sannu Sannu Akeyin Sa Ba Kamar Barna Ba .Wannan Aikin Yana Da Matukar Yawa Kama Daga Yin Hanya Daga Cibiyar Ruwa Wato ( Gubi Dam ) Da Sauran Yin Wayarin Izuwa Cikin Gari Amma Insha Allah Nan Da Wasu Lokuta Matsalan Ruwan Sha Zaizama Tarihi A Cikin Garin Bauchi Harma Da Sauran Kananun Hukumo Min Da Muke Dasu A Jihar Bauchi .

Mu Cigaba Dayiwa Mai Girma Gwamnan Jihar Mu Ta BAUCHI Addu’an Allah Yabashi Ikon Sauke Nauyin Daya Rataya Akansa .Allah Yabashi Sa’a Wajen Ciyar Da Jihar Bauchi Gaba Ameen .

Mu’azu Sakwa
31/3/2021
©️ Kaura Media Team.

Please follow and like us:

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.