(HAUSA) Musa Azare ya rawaito: Zuwa Ga ‘Yan Kungiyar Kare Muradun Tsohuwar Gwamnatin Da Nake Alfahari Da Bayar Da Gudummawa Wajen Kifar Ta;

Da fatan kun kwana lafiya. Kamar yadda kuke ta cecekuce akai na, cewar naki nayi magana akan wata kwangila da ake zargin gwamna mai ci Bala Mohammed ya baiwa wani kamfani da ake zargin shi darakta ne a kamfanin.

Saqo na gareku shine, duk ranar da kukayi wa al’ummar jihar Bauchi bayani akan dalilan da yasa kukayi ta bada kariya (ba ma kukayi shiru kawai ba), wa tsoffin iyayen gidan ku yayin da;

1. Naira biliyan 2.3 tayi batan dabo wajen bisine gawawwaki a jihar mu.

(Yan kwangilar dai sun shaida mana cewa basu san ma an fitar da kudaden da sunan su ba).

2. Yadda takaktoci 460 daga cikin 500 da aka laqume kudaden su, suka gagara isowa jihar mu har kuka kife.

(Dan kwangilar dai ya shaida mana a kwamiti cewa shi bai ci ko anini ba daga cikin kudaden).

3. Yadda kudade kumani naira biliyan 6 suka salwanta da sunan aikin hanyar Federal Lowcost, kuma ba’a yi aikin ba.

(ita ma wannan dan kwangilar yayi mana bayanin yadda akayi, yayin da ya gurfana a gaban mu).

4. Yadda mai gidan ku ya fitar da kudade kumanin naira miliyan 418 da sunan wani kamfani (Wurosoyo), ana dab da zaben 2019, wai domin ayi feshin kwari a makarantun firamare na jihar Bauchi. Feshin da kowa yasan ba’a yiba.

5. Yadda mai gidan ku ya kashe kudade sama naira biliyan 8.5 kwana biyu kafin ya miqa mulki.

6. Yadda akayi tarakta har guda hudu suka buya a gidan Oga, bayan kuma bashi da gona a Najeriya sai a jamhuriyar Czechs. Yanzu haka mun kwato wadannan taraktoci, amma dai ina son kuyi bayani duk da haka.

7. Yadda mai gidan ku ya saida ma kansa gidan gwamnati a farashi mai rahusa, kuma ba tare da bin qa’idar doka ba.

8. Yadda mai gidan ku ya saida ma kansa motoci na alfarma wadanda kudaden su yakai kimanin naira miliyan 600, akan kudi naira miliyan 7 da dan doriya.

9. Yadda wani kamfani mai suna Haitrix ya rinqa samun kwangiloli na daruruwan miliyoyin nairori, kwana biyar kachal bayan kafa shi. Wannan kamfani kuma na ‘ya’yan tsohon babban akanta jihar mu ne, su kuma aminai ne ga ‘ya’yan Oga. An kafa wannan kamfani kwana biyar kachal bayan nada wancan babban akanta na jihar mu a shekarar 2015.

10. Yadda dalar Amurka miliyan guda tayi batan dabo a ma’aikatar ilmi ta jihar Bauchi. Wannan dala, tana daga cikin kudaden da babban bankin duniya ya baiwa jihar Bauchi a matsayin kudin tallafawa ilmin ‘ya’yan talakawa.

11. Yadda kudaden aikin hanyar Bulkachuwa zuwa Udubo, Udubo zuwa Gamawa, suka shiga.

12. Yadda kudaden aikin hanyar Gafchiyari suka shiga. Yadda kudaden aikin Atahowa suka shiga. Wadannan, dama wasu da dama da zasu biyo baya nan ba da dadewa, sai kunyi min bayani tukunna, kafin na fito na fadi abinda kuke son ji daga baki na, game da waccar kwangila.

Daga nakun nan dai wanda yayi sanadiyyar kifewar ku, Malam Musa Azare 26 Fabrairu, 2020

One thought on “(HAUSA) Musa Azare ya rawaito: Zuwa Ga ‘Yan Kungiyar Kare Muradun Tsohuwar Gwamnatin Da Nake Alfahari Da Bayar Da Gudummawa Wajen Kifar Ta;

  • February 26, 2020 at 1:16 pm
    Permalink

    Wadannan tambayoyi da sauran masu zuwa basu da amsa sai dai suyi zagi wanda a kullum ita ce dabiar marasa gaskiya

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

WhatsApp chat